Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Zanga zangar wacce akayi a daidai zagayowar ranar tarukan ranar nuna goyon baya ga al’ummar Falastinu wacce ta gudana a jiya 29 ga wayan Nuwamba.
Yau shekara guda kenan da Morocco ta dawo da alakarta da Isra’ila, a cikin tsarin yarjejeniyar nan Abraham ta gwamnatin Amurka mai manufar daidaita alaka tsakanin Isra’ila da kasashen larabawa.
Majalisar Dinkin Duniya dai ta ayyana ranar 29 ga Nuwamba a matsayin ranar duniya ta hadin kai da nuna goyon baya ga al'ummar Falasdinu.
A ranar 29 ga watan Nuwamban shekarar 1977 Majalisar Dinkin Duniya ta amince da wannan rana, tare da yin kira ga kasashe mambobinta da su sanya wannan rana a cikin kalandarsu da kuma raya ta a kowace shekara.
342/